Babu ja: Sai mun kawowa Buhari Kwara – Lai Mohammed

Babu ja: Sai mun kawowa Buhari Kwara – Lai Mohammed

Ministan bayanai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, yace babu ja da baya wajen kawowa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da shugaban kasa Muhammadu Buhari Kwara a zaben 2019.

Ministan a wata sanarwa da ya saki a Abuja a ranar Litinin, ya bayyana cewa sauya shekar da yan majalisa suka yi kwanan nan, mambobin APC da magoya bayanta a Kwara sun jajirce domin karfafa jam’iyyar.

Babu ja: Sai mun kawowa Buhari Kwara – Lai Mohammed

Babu ja: Sai mun kawowa Buhari Kwara – Lai Mohammed

Yace jam’iyyar zata bude kofofinta ga wadanda suke son shiga jam’iyyar da kuma gyare-gyare gabannin zaben 2015.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Tsoffin shugabannin kasa Obasanjo da Jonathan sun yi ganawar sirri

Ministan ya bayyana cewa da sauya shekar yan majalisar dokoki na APC, toh an raba alkamarsu daga dusa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel