EFCC ta kama wani gwamna a arewa ya cinye sama da naira biliyan 20

EFCC ta kama wani gwamna a arewa ya cinye sama da naira biliyan 20

A jiya ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa wato (EFCC), ta ce an barnatar da kudi sama da naira biliyan 20 a karkashin kulawar gwamnan jihar Benue Samuel Ortom

EFCC ta kama wani gwamna a arewa ya cinye sama da naira biliyan 20

EFCC ta kama wani gwamna a arewa ya cinye sama da naira biliyan 20

A jiya ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa wato (EFCC), ta ce an barnatar da kudi sama da naira biliyan 20 a karkashin kulawar gwamnan jihar Benue Samuel Ortom.

Wani babban jami’in hukumar ta EFCC wanda yayi magana da manema labarai, ya bayyana cewa sun samu nasarar binciko hakan ta dalilin rahoton da aka kai musu na barnatar da kudi da ake yi a jihar.

Masu binciken sunce sun samu kudi sama da naira biliyan 20 wadanda aka cire daga asusun gwamnan jihar har guda hudu, daga watan Yulin shekarar 2015 zuwa watan Maris na wannan shekarar.

DUBA WANNAN: Ruwa ba ya tsami banza: Da hannun tsofin gwamnonin PDP a rikicin makiyaya da manoma – Binciken Turai

Hukumar ta ce ta samu asusu guda biyu wadanda aka bude su da sunan gwamnan jihar. Ta kara da cewa an tura sama da naira biliyan 1.9 a tsakanin watan Yulin shekarar 2015 zuwa watan Maris din wannan shekarar. Hukumar tace bayanai sun nuna cewa wasu manyan jami’an gwamnatin jihar guda 3 wadanda suka hada da Emmanuel Aorga, Patrick Abah da kuma Ochaja Peter - sun cire kudi a lokuta da dama daga cikin asusun.

Wasu asusu kuma da aka bude su da sunan ‘Bureau for Internal Affairs da kuma Special Services Accounts’ tsakanin shekarar 2015 zuwa wannan shekarar da muke ciki, bayanai sun nuna cewar, asusun sun karbi kudi sama da naira biliyan 19 daga hukumar FAAC.

Hukumar ta ce wani babban jami’in gwamnatin jihar mai suna Oliver Mtom, shine ya cire duka kudaden, inda ta kara da cewa yana cire kudin duk wata da zarar hukumar FAAC ta turo kudin. Inda daga baya hukumar ta gano cewar kudaden ana kaiwa wasu Sakatarorin jihar ne.

Hukumar ta gayyaci babban Sakataren jihar Gabriel Iangba, inda aka tambaye shi kudin asusun gidan gwamnatin jihar; Iangba ya bayyanawa hukumar EFCC cewar an kashe kudin ne a fannin masu tsaron lafiyar gwamnan jihar, hidindimun gidan gwamnatin jihar, tafiye-tafiye da kuma kayan abinci.

Shi kuma Sakatare Boniface Nyaakor da aka tambayeshi akan kudin sauran asusun guda biyu, ya bayyana cewar an rabawa hukumomin gwamnatin jihar ne guda 6.

Daga baya hukumar EFCC ta samu bayanin cewar gwamnan yana kone duk wata shaida da zata bada damar bayyana wuraren da aka rarraba kudaden.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel