Inyamurai: Kafin in bar mulki sai an yi maku hanyoyi – Shugaba Buhari

Inyamurai: Kafin in bar mulki sai an yi maku hanyoyi – Shugaba Buhari

- Gwamnatin Buhari ta yi alkawarin gyara hanyoyi da ke kasar Inyamurai

- Shugaba Buhari ya shimfida wani titi a Garin Isieketa da ke Jihar Abiya

Labari ya zo mana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya fito ya bayyana irin tanadin da yake yi wa Kasar Inyamurai. Mai magana da yawun Shugaban kasa watau Femi Adesina ne yayi wannan jawabi.

Inyamurai: Kafin in bar mulki sai an yi maku hanyoyi – Shugaba Buhari
Shugaba Buhari yace kafin ya bar ofis zai yi wa Inyamurai kokari

Femi Adesina wanda ya wakilci Shugaban kasar a wajen wani biki da aka yi na shimfida wata hanya a cikin Garin Isieketa da ke karamar Hukumar Ngwa ta Kudu a Jihar Abia. Hukumar NNDC mai kula da Neja-Delta ce ta yi wannan aiki.

KU KARANTA: Sanata Kwankwaso ya kara samun gindin zama a Jam’iyyar PDP

Gwamnatin Shugaba Buhari ta koka da yadda hanyoyi na titi su ka mutu musamman kafin kafa Gwamnatin APC a kasar nan. Shugaban kasa Buhari yace zai yi bakin kokari wajen ganin cewa an gyara hanyoyin da ke cikin Najeria kafin ya bar mulki.

Shugaban kasan ya nuna cewa kafin ya kammala wa’adin sa, sai ya gyara bangaren na Inyamurai da ke Kudancin kasar. Shugaba Muhammadu Buhari ta bakin mai magana da yawun sa yace nan gaba Kudancin kasar za ta canza sarai ba kamar da ba.

Femi Adesina wanda ke ba Shugaban kasar shawara kan harkokin yada labarai ya bayyana cewa maganar titi da dogo na jirgin kasa da wutan lantarki ne a gaban Shugaba Buhari. Mutanen Yankin sun yabawa kokarin wannan Gwamnatin ta APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng