Arzikin Najeriya: Jerin Jihohin da ke gaba wajen iya tatso kudi a kasar nan

Arzikin Najeriya: Jerin Jihohin da ke gaba wajen iya tatso kudi a kasar nan

Mun kawo maku Jihohin da su ka fi kowane iya samun kudin shiga a halin yanzu a Najeriya. Da dama dai daga cikin Jihohi su na dogara ne da Gwamnatin Tarayya domin ba su da karfin cikin gashin kan su ta fuskar tattalin arziki.

Jerin Jihohin da ke gaba wajen iya tatso kudi a kasar nan

Ko babu kudin Gwamnatin Tarayya Legas za ta zauna da kafafun ta

A shekarar nan dai, ga abin da alkaluman Hukumar NBS na kasa ta nuna:

1. Legas

Jihar Legas ce kan gaba idan ana maganar iya samun kudin shiga a Najeriya. Alkaluman kasar sun nuna cewa Legas na iya samun sama da Naira Biliyan 250 da kan ta a shekara ko da babu cin bashi ko kuma dogaro daga Gwamnatin Tarayya.

KU KARANTA: Wani Attajiri ya rasa abin da ya fi karfin dukiyar Dangote a kwana 2

2. Delta

Bayan Legas kuma wanda ke gaba sai Jihar Delta wanda ke can baya. A Jihar Delta da mutane ba su wuce Miliyan 4 ba ana iya samun sama da Naira Biliyan 40 a kowace shekara. Delta na Kudu maso Kudancin Kasar ne kuma ta na da mai.

3. Ogun

Ogun da ke makwabtaka da Legas ce ke bin Delta daf a baya. Yanzu haka Jihar Ogun na iya dagewa ta hada sama da Naira Biliyan 30 a kowace shekara. Kusan bayan Legas, Jihar Ogun ta fi kowace Jiha yawan manyan kamfanoni da masana’antu.

Za dai ku lura cewa babu Jihar Arewa ko daya cikin Jihohin da su ke more kudin shiga watau IGR. Kano ta zo ne a ta 10 a wannan jeri. Abin da Kano wanda ta fi kowace Jiha arziki a Arewa ta ke samu a shekara ya kan haura Naira Biliyan 13 a halin yanzu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel