An yi ca a kan Sanata Kwankwaso bayan an gan shi tare da Femi Fani-Kayode

An yi ca a kan Sanata Kwankwaso bayan an gan shi tare da Femi Fani-Kayode

A farkon makon nan ne aka samu labari cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da wani tsohon Ministan sufuri da kuma al'adu na kasar nan watai Femi Fani-Kayode.

An yi ca a kan Sanata Kwankwaso bayan an gan shi tare da Femi Fani-Kayode

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya zauna da Fani Kayode

Sai dai mutane da dama musamman ‘Yan Arewa ba su ji dadin ganin tsohon Gwamnan a gidan Femi Fani-Kayode ba. Fani-Kayode mutum ne dai da aka yi masa tambari da suka da tsanar Musulmai musamman Fulani a Najeriya.

Rabiu Kwankwaso wanda bisa dukkan alamu zai nemi takarar Shugaban kasa a zaben 2019 ya gana ne da tsohon Ministan na PDP a gidan sa. Sanatan bai bayyana cewa sun zauna da ‘Dan PDP ba amma dai maganar ta fito fili daga baya.

KU KARANTA: Buhari zai gana da wani Bawan Allah da ya ceci mutum 300 a rikicin Jos

Har yanzu dai Sanatan na Kano ta tsakiya bai bayyana makusudin zaman da yayi da tsohon Ministan ba, sai dai bai rasa nasaba da 2019. A cikin kwanakin nan Kwankwaso ya gana da Ibrahim Shekarau, Babangida Aliyu da Sule Lamido.

Har wasu Magoya bayan fitaccen Sanatan watau Rabiu Kwankwaso da ke Kudancin Kasar nan dai wannan zama bai masu dadi ba saboda sun a ganin Fani-Kayode rikakken Makiyin Gwamnatin Buhari ne kuma mai sukar addinin Musulunci.

Dma kun ji labari cewa Abdullai Sani Rogo wanda tsohon Kwamishinan Jihar Kano ne kuma wanda yayi takarar kujerar Gwamna a 2011 da Sanata a 2015 yayi murnar dawowar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Magoya bayan sa cikin PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel