Kallabi tsakanin rawuna: Jinin sarautar Kano ta bayar da mamaki a jami’ar Turai, ta lashe kyautar duniya

Kallabi tsakanin rawuna: Jinin sarautar Kano ta bayar da mamaki a jami’ar Turai, ta lashe kyautar duniya

Zuwaira Hashim, matashiya mai shekara 20 daga gidan sarauta a jihar Kano ta bayar da mamaki a jami’ar Sheffield ta kasar Ingila bayan ta fita da sakamako mafi kyau a karatun digiri da ta kamma wannan watan a bangaren “Biomedical Science Health and Human Sciences”.

Zuwaira ta kasance daliba mafi karancin shekaru a ajinsu amma kuma duk da haka ta doke ragowar daliban ta fuskar samun sakamako mafi kyau. Hakan ya saka ta lashe kyaututtuka da dama da suka hada da ta “Kerry Ann Salt Memorial Prize” da “Global Engagement Award”.

Kallabi tsakanin rawuna: Jinin sarautar Kano ta bayar da mamaki a jami’ar Turai, ta lashe kyautar duniya

Zuwaira Hashim

Zuwaira ta yi bincikenta na shekarar karshe a kan yadda za a yi kiyaye kamuwa tare da dakile yaduwar ciwon sukari.

Yanzu haka Zuwaira ta dawo gida Najeriya domin hidimtawa kasa (NYSC) kamar yadda doka tayi tanadi ga duk dan kasa day a kamala digirin farko kuma bai wuce shekara 30 da haihuwa ba.

DUBA WANNAN: An kama na hannun daman Jonathan da laifin shirga karya da yada labaran bogi, duba shaida

Wannan ba shine karo na farko da wani dalibi daga Najeriya ya nuna hazaka ta ban mamaki a jami'ar kasashen Turai ba, sai dai kawai abin da ya fi burguwa a lamarin Zuwaira shine karancin shekarunta

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel