Shehu Sani yayi martani akan mamayar da aka kai majalisar dokokin Benue

Shehu Sani yayi martani akan mamayar da aka kai majalisar dokokin Benue

Dan majalisa mai wakiltan yankinKaduna ta tsakiya a majalisar dokokin kasar Sanata Shehu Sani ya maida martani ga zargin mamayar da aka kai majalisar dokokin Benue.

Sanatan wadda ya bayyana hakan a sahfinsa na Twitter a ranar Litinin, 30 ga watan Yuli, yace ya zama dole a bi umurnin kotu akan wannan lamari sannan kuma a mutunta hakkin kowani dan Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Sanatocin da suka sauya sheka masu aikata rashawa ne, kuma suna tsoron a kama su idan Buhari ya sake cin zabe – El-Rufai

A baya Legit.ng ta rahoto cewa tsohon gwamnan jihar Kadiuna, Balarabe Musa, yace shi bai ce kada Shehu Sani ya bar APC amma kada ya koma jam’iyyar Peoples Democratic Party.

Shehu Sani ya bayyana cewa Musa, shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole da Bola Tinubu na daga cikin wadanda suka rarrashe shi da kada ya bar APC zuwa jam’iyyar adawa, PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel