Kiri – kiri: An kama na hannun daman Jonathan da laifin aikata karya da yada labaran bogi, duba shaida

Kiri – kiri: An kama na hannun daman Jonathan da laifin aikata karya da yada labaran bogi, duba shaida

A yayin da ake cigaba da nuna yatsa da tone-tone tsakanin ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP da kumai mai mulki, APC, Reno Omokri, daya daga cikin hadiman tsohon shugabankasa Goodluck Jonathan ya sha kunya a dandalin sada zumunta na Tuwita bayan ya yi amfani da labarin karya domin sukar gwamnati.

Omokri na daya daga cikin ‘yan sahun gaba wajen sukar manufofi da tsare-tsaren jam’iyyar APC da gwamnatinta karkashin jagorancin shugaba Buhari.

A wannan karon, Omokri, ya yada a shafinsa na Tuwita cewar hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta saki alkaluman dake tabbatar da cewar mutane miliyan 7.9 sun rasa aiyukansu a cikin watanni 21 tare da sukar gwamnati cewar ta gaza samar da aiyuka ga mutane, hasali ma sai jawowa mutane asarar aiyukansu take yi.

Kiri – kiri: An kama na hannun daman Jonathan da laifin aikata karya da yada labaran bogi, duba shaida

Reno Omokri

Kiri – kiri: An kama na hannun daman Jonathan da laifin aikata karya da yada labaran bogi, duba shaida

Yadda aka kama Reno kir-kiri da aikata karya da yada labaran bogi

Bayan Omokri ya yada wannan labari ne sai shugaban hukumar NBS, Dakta Yemi Kale, ya mayar masa da raddi kan cewar hukumarsa bata saki wani labari ko rahoto mai alaka da hakan ba.

DUBA WANNAN: Da hannun tsofin gwamnonin PDP a rikicin makiyaya da manoma - Rahoton binciken kungiyar Turai

Kale ya kara da cewar tun shekarar 2007 rabon da hukumar NBS ta saki wasu alkaluma dangane da batun aikin yi. Kazalika ya bukaci Omokri ya nesanta hukumar NBS daga harkokinsa na siyasa musamman amfani da sunanta domin yada labaran karya.

Shugaban na NBS bai tsaya iya haka ba sai da ya sanar da sanar da Omokri cewar ba zasu taba ganin mai kokarin siyasantar da aikinsu da kima ko mutunci ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel