Atiku yayi magana akan makircin da ake shiryawa na tsige Gwamnan Benue, Samuel Ortom

Atiku yayi magana akan makircin da ake shiryawa na tsige Gwamnan Benue, Samuel Ortom

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi Allah wadai da lamarin siyasar dake wakana a jihar Benue inda yan majalisa na jam’iyyar All Progressives Congress ke kokarin tsige Gwamna Samuel Ortom.

Yan majalisan na APC sun gabatar da takardar sanar da batun tsige Gwamna Ortom bayan sun zarge shi da aikata rashawa.

Da yake maida martani ga lamarin a wata sanarwa a ranar Litinin a Abuja, tsohon mataiakin shugaban kasar yace wasar kwaikwayon siyasar jihar Benue ya bashi kunya matuka.

Ya yi Allah wadai da makircin na son tsige Mista Ortom sabanin abunda kundin tsarin mulkin kasar ta gindaya.

Atiku yayi magana akan makircin da ake shiryawa na tsige Gwamnan Benue, Samuel Ortom

Atiku yayi magana akan makircin da ake shiryawa na tsige Gwamnan Benue, Samuel Ortom
Source: Depositphotos

A cewarsa duk wani yunkuri na take kundin tsarin mulki da shari’a wajen tsige wani gwamna alamu ne na juyin mulki kuma kamata a yi hukunci kan haka.

Atiku ya bayyana cewa jihar Benue dake fuskantar matsalar rashin tsaro a yanzu, duk wani yunkuri na tsige gwamna ba bisa ka’ida ba zai sake tabarbarar da lamura ne.

KU KARANTA KUMA: Sanatocin da suka sauya sheka masu aikata rashawa ne, kuma suna tsoron a kama su idan Buhari ya sake cin zabe – El-Rufai

Ya bukaci yan sanda da su zamo a tsakiya sannan su guje ma duk wani kokari na amfani da su a lauran siyasa domin kare martabar hukumar yan sanda.

Ya kara da cewa biyayyar yan sanda ya kamata ya zamo akan doka da kundin tsarin mulki ne.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel