Dalilin da ya sa ya zama dole mu tsige Ortom Mun – Hon Ikyange

Dalilin da ya sa ya zama dole mu tsige Ortom Mun – Hon Ikyange

Kakakin majalisar dokokin jihar Benue da aka tsige, Terkimbir Ikyange ya bayyana a ranar Litinin cewa sun majalisar ta fara yunkurin tsige Gwamna Samuel Ortom.

Hakan na zuwa ne bayan wata kungiyar gamayyar yan majalisa karkashin sabon kakakin majalisa, Hon. Titus Uba sun bayyana cewa sun dakatar da Ikyange da mukarrabansa na tsawon watanni shida.

Dalilin da ya sa ya zama dole mu tsige Ortom Mun – Hon Ikyange

Dalilin da ya sa ya zama dole mu tsige Ortom Mun – Hon Ikyange

Da yake Magana da manema labarai a gidansa bayan zamana majalisa, Ikyange ya bayyana cewa majalisa zata zanta akan wasikar tsige gwamnan nan da kwanaki 7.

KU KARANTA KUMA: Labari mai dadi: An dawo da aiki gadan-gadan a gadar Loko-Owoto wadda ke sada Benue da Nasarawa (hotuna)

A ranar Litinin ne mabobin majalisa goma sha biyu da Ikyange ke jagoranta suka isa majalisa cike da matakan tsaro.

Ya zargi Ortom da yin sama da fadi a kudaden jiha kimanin Naira biliyan 55.

Ya bayyana cewa Ortom yayi sama da fadi da naira biliyan 33 ta hanyar rage kudaden karamar hukua da kuma amfani da wasu naira biliyan 22 wajen siyayya ga jam’iyyar siyasa kafin ya sauya sheka zuwa PDP.

A cewar Ikyange, sakamakon haka ya sa kudin biyan ma’aikatan jihar ya shiga wani yanayi inda ma’aikatan gwanatin jiha ke bin albashin watanni bakwau, kananan hukumomi na bin watanni 1 sannan yan fansho na bin watanni 14.

Yace yunkurin tsige Ortom na da nasaba da gazawar gwamnatinsa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel