Yanzu-yanzu: An tsige mataimakin gwamnan jihar Imo

Yanzu-yanzu: An tsige mataimakin gwamnan jihar Imo

Rahoton da shigowa da dumi-dumi na nuna cewa yan majalisan dokokin jihar Imo sun tsige mataimaki gwamnan jihar, Eze Madumere.

Tashar Channels ta bada rahoton cew mambobi 19 cikin 37 na majalisan ne suka tsige shi.

A kwanakin bayam majalisar ta samu rahoton kwamitin binciken da babban alkalin jihar ya nada akan mataimakin gwamnan.

Mr Madumere ya kasance cikin rikicin siyasa da maigidansa gwamnan jihar, Rochas Okorocha akan wanda za’a maye gurbin Okorocha bayan kare wa’adinsa.

Yayinda Eze Madumere ko sha’awar hawa kujeran Okorocha, gwamnan ya bayyana niyyar daura sirikinsa.

Rikici ya yi zurfi wanda ya sabbaba rabuwan kai tsakanin mambobin jam’iyyar APC a jihar Imo inda suka rabu gida biyu.

Wani sashe karkashin jagorancin sakataren jam’iyyar ta kasa, Osita Izunaso, na goyon bayan mataimakin gwamnan, dayan bangaren kuma karkashin jagorancin gwamnan jihar, Rochas Okorocha.

Jihar Imo ta halarci taron gangamin jam'iyyar APC da akayi a Abuja kansu a rabe. Amma a karshe taron, bangaren gwamnan sun samu nasara inda suka samu damar kayar da sakataren jam'iyyar ta kasa a zaben. Tun daga lokacin aka fara yunkurin tsige mataimakin gwamnan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel