Aiki ko aika-aika: Wasu a Gwamnatin Ganduje sun fara tono badakalar Kwankwaso

Aiki ko aika-aika: Wasu a Gwamnatin Ganduje sun fara tono badakalar Kwankwaso

Mun ji labari cewa daya daga cikin masu ba Gwamnan Kano Dr. Umar Abdullahi Ganduje shawara ya tona asirin wasu badakaloli na tsohon Gwamnan na Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Salihu Tanko Yakassai wanda ya ke ba Gwamna Abdullahi Ganduje shawara kan harkokin yada labarai ya tabbatar mana da cewa Gwamnatin tsohon Gwamna Kwankwaso ta tafka aika-aika iri a tsakanin 2011 zuwa 2015 da tayi mulki.

Ganduje

Wani na-kusa da Gwamna Ganduje ya zargi Kwankwaso da aika-aika

Tanko Yakasai wanda a da yake yabon Kwankwaso ya fito ya bayyana abin da ya sani game da Gwamnatin tsohon Gwamnan bayan ya shiga Gwamnati. Yakassai yace Kwankwaso ya tafi ya bar ‘Yan kwangila da tarin bashi.

A cikin fallasar da Yakassai yayi yana cewa:

"Wani dan kwangila bashin banki ya ci yai aikin, wani kadarar sa ya siyar, wani dukiyar sa ya diba ya saka, ashe duk gadar zare ce aka shirya musu. Saboda zalunci alaji. Allah kadai Ya san iyaka”

KU KARANTA: Ministan Buhari ya ji dadin barin su Kwankwaso APC

Mai ba Gwamnan shawara yace akwai Gada ta Gadon Kaya da aka kashewa Biliyan 2 sai dai har gobe Gwamnatin Kwankwaso ba ta biya kudin wannan aiki ba. Har wa yau, Yakassai yace akwai wasu kudin ‘Yan makaranta da aka cinye.

Akwai wasu ayyukan kamar wanda su ka hada da titin Sabuwar Kofa da na Miyangu wanda ba a biya ‘Yan kwangilar kudin aikin su ba. Malam Salihu Tanko Yakassai yace wata sharia’ar sai a lahira za ayi da tsohon Gwamnan Jihar.

Kwanan nan ne tsohon Gwamnan ya bar APC ya koma PDP inda har yayi wani zaman kus-kus a cikin dare tsakanin sa da Malam Ibrahim Shekarau. Kwankwaso ya samu sabani da tsohon Mataimakin sa wanda yake Gwamna yanzu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel