Sauyin sheka ya bayyana mana Munafukan boye - Ministan yada labarai Lai Mohammed

Sauyin sheka ya bayyana mana Munafukan boye - Ministan yada labarai Lai Mohammed

Mun samu labari cewa Ministan yada labarai da kuma al’adu watau Lai Mohammed yayi magana game da ‘Yan Majalisar Tarayyar da su ka fice daga Jam’iyyar APC su ka sheka zuwa PDP kwanan nan.

Sauyin sheka ya bayyana mana Munafukan boye - Ministan yada labarai Lai Mohammed

Bangaren Saraki a Kwara sun fice daga APC sun koma PDP

Alhaji Lai Mohammed yace yanzu an yi walkiya sun gane munafukan Jam’iyyar tun asali. A cewar Ministan Kasar yanzu an yi rairaye ne da tankada sun gane ‘Yan Jam’iyyar APC na asali da kuma bara-gurmin da ake tafiya da su.

Ministan na Najeriya yayi wannan jawabi ne a karshen makon nan lokacin da ya ziyarci Jihar Kwara inda yace sun ji dadin yadda Munafukan cikin APC su ka fice. Ministan yace duk wannan ba zai hana APC cin zaben ta ba a badi.

KU KARANTA: Dr. Usman Bugaje ya bayyana abin da ya sa ake barin APC

A karshen makon jiya ne ‘Yan Majalisa kusan 50 su ka koma PDP. Daga cikin ‘Yan Majalisar Kasar da su ka bar APC su ka koma PDP akwai kusan mutum 10 wanda Ministan yake gani su ne su ka hana ruwa guda a Jihar Kwara.

Lai yayi murnar cewa yanzu za su karbe Jam’iyyar APC a Jihar Kwara su yi mata garambawul. A cewar Ministan, sun dade su na addu’ar Allah ya kawo ranar da wadanda su ka sauya shekan za su fice daga Jam’iyyar APC mai mulki.

Kwanaki kun ji cewa Jam’iyyar PDP tana kulla damarar lashe zabe a Jihar Oyo inda APC ke da karfi. Jihar Oyo ta na kusa da Jihar Kwara ne kuma Jam’iyyar APC ta sake rasa wasu ‘Ya ‘yan ta a can kwanan nan zuwa Jam’iyyar adawa ta PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel