Ba kanta: An dakatar da ‘yan majalisar da suka yi yunkurin tsige gwamnan Benuwe

Ba kanta: An dakatar da ‘yan majalisar da suka yi yunkurin tsige gwamnan Benuwe

- 'Yan majalisar ta su kayi yunkurin sauke gwamnan Benuwe daga kujera sun gamu da gamonsu

- Bayan gazawar yunkurin nasu an dakatar da su har tsawon watanni shida

- Wannan na zuwa bayan gwamnan jihar ta Benuwe Samuel Ortom ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

Majalisar dokokin jihar Benue ta dakatar da 'yan majalisunta takwas bisa yunkurin tsige gwamnan jihar Samuel Ortom.

Ba kanta: An dakatar da ‘yan majalisar da suka yi yunkurin tsige gwamnan Benuwe

Ba kanta: An dakatar da ‘yan majalisar da suka yi yunkurin tsige gwamnan Benuwe

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa ‘yan majalisun wadanda ‘yan jam'iyyar APC ne sun shiga zauren majalisar ne domin kawo batun tsige gwamnan, a sanadin hakan ya janyo musu hukuncin dakatarwa har na tsawon watanni shida.

KU KARANTA: Iyalan Dasuki sun kai ministan shari'a AGF Malami kara

'Yan majalisun da ake zargi da aikata wannan laifi sun hada da; Adanyi Benjamin, Terhemba Chabo, Benjamin Nungwa, Bem Mngutyo, Adams Okloho, James Okefe da kuma Nick Eworo.

‘Yan majalisun sun samu jagorancin shugaban majalisar Terkimbi Ikyange, wanda tuni gwamnatin jihar ta dakatar da shi shima.

Shi kuwa Gwamna Ortom, kamar yadda mai magana da yawunsa ya bayyana a cikin wani jawabi ya ce ‘yan majalisun basu da ikon tsige gwamnan saboda basu cika dokokin yin hakan ba.

Ya kara da cewa ba su biyo hanyar da ta dace ba, ta yin amfani da kundin tsarin mulki ko kuma amfani da shari'a wajen aiwatar da kudurin nasu.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel