Batun tumbuke Ortom: Gwamnan jihar Benue ya mayar da martani ga yan majalisa

Batun tumbuke Ortom: Gwamnan jihar Benue ya mayar da martani ga yan majalisa

Gwamnan jihar Benuwe Samuel Ortom ya yi watsi da yunkurin tsige shi daga mukamin gwamna da wasu yan majalisun dokokin jihar daga jam’iyyar APC su takwas suka yi, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakakin gwamnan, Terver Akase ne ya bayyana haka a madadin gwamnan, inda ya tabbatar da cewa har yanzu Samuel Ortom ne gwamnan jihar Benue, kuma wannan mataki da yan majalisan suka dauka ya saba ma Doka.

KU KARANTA: Na rasa abinda na yi, sau 4 ina tsallake harin yan bindiga a shekarar nan – Dino Melaye

“Ortom ne gwamnan jihar Benuwe mai cikakken iko har yanzu, babu yadda za’a yi ku tsige gwamna faraddaya ba tare da bin ka’idojin da doka ta tanadar ba, ko da suke wannan maganan basu kai adadin da doka ta yanke ba, don haka ba zai yiwu ba.

“Yan majalisa takwas ne kacal suka aika ma gwamnan da takardar tsigewa, haka zalika mutum biyu daga cikin wadanda suka dauki wannan mataki mutanen gwamna ne, don haka ta yaya za’a kira wannan takarda ta tsige gwamna.” Inji shi.

Daga karshe Terver ya bayyana lamarin gaba daya a matsayin dariya, wanda ya bai kamata jama’a su dauke da muhimmanci ba, ya kara da cewa a yanzu haka akwai hukuncin Kotu da ta hana korarren Kaakakin majalisa dokokin jihar daga bayyana kansa a matsayin Kaakaki.

“Majalisa ta dakatar da mutumin nan na tsawon watanni shida, don haka bas hi da wata dama ko ikon komawa majalisar har sai bayan wa’adin da aka tanadar masa.” Inji Kaakakin gwamnatin jihar Benuwe.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel