Na rasa abinda na yi, sau 4 ina tsallake harin yan bindiga a shekarar nan – Dino Melaye

Na rasa abinda na yi, sau 4 ina tsallake harin yan bindiga a shekarar nan – Dino Melaye

Dan majalisa mai wakiltar al’ummar jihar Kogi ta yamma a majalisar dattawan Najeriya, Sanata Dino Melaye cewa a cikin shekarar 2018 kadai ya gamu da harin yan bindiga har sau hudu, inda yace amma Allah ya taimakeshi ya tsallakesu duka ba tare da maharani sun samu nasarar halaka shi ba, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Melaye ya kara da cewa hukumar Yansandan Najeriya ta janye Yansandan dake gadinsa, duk kuwa da cewa ya bi akan su dawo masa da masu gadin lafiyar tasa, hatta majalisar dattawa ya baiwa hukumar Yansanda umarnin yin hakan amma hukumar ta yi biris dasu.

KU KARANTA: Zakarar da Allah ya nufa da cara: Wata yarinya ta tsere daga hannun mayakan Boko Haram

Na rasa abinda na yi, sau 4 ina tsallake harin yan bindiga a shekarar nan – Dino Melaye

Dino Melaye

Meleya ya bayyana haka ne a lokacin da yake bada labarin yadda aka yi kokarin kashe shi a ranar Alhamis, 19 ga want Yuli akan hanyarsa zuwa jihar Kogi don halartar zaman kotu bisa kara da aka shigar da shi kan mallakar makamai ba akan ka’ida ba.

“Ina kan hanyar zuwa Kogi sai naga wata mota kirar Sianna tana biye dani a baya, zuwa can sai ta sha gabana, ta tare min hanya, sa’annan wasu daga cikin mota suka bude min wuta, da kyar na fita daga mota, na yi cikin daji a guje.

“Ina shiga dajin sai na dare kan wata bishiya, ina nan na hangi wasu yan bindiga guda biyu sun biyo ni cikin dajin suna farautar rayuwata, amma Allah bai basu ikon gani na ba a saman bishiya, sai da kwashe awa goma sha daya akan bishiyar, kafin na fito. Allah ne ya kare ni.” Inji shi.

Daga karshe Melaye ya musanta zargin mallakar makamai da ake yi masa, inda yace gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ne ya kulla masa sharri da hadin bakin hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, sa’annan yace janye jami’an Yansanda dake gadinsa ya sanya shi hadari.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel