Sauya sheka: PDP na yiwa Saraki, Tambuwal da Ahmed tanadi na musamman

Sauya sheka: PDP na yiwa Saraki, Tambuwal da Ahmed tanadi na musamman

Jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP a wannan mako ta yi shirin tarba tare da bikin masu sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress, APC mai mulki, biki gagarumi.

A nata bangaren, jam’iyyar APC, a jiya ta bayyana cewa ta kammala shirye-shirye domin ganin ta dawo da matsayarta ta hanyar kwato wasu manyan jiga-jigan PDP.

An tattaro cewa taron tarban masu sauya shekar na iya kasancewa tare da sauya shekar Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto, Gwamna Abdulfatah Ahmed na jihar Kwara da kuma wasu manyan jiga-jihan jam’iyyar ta APC. Ba’a riga an san takamaman ranar sauya shekar shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ba.

Sauya sheka: PDP na yiwa Saraki, Tambuwal da Ahmed tanadi na musamman

Sauya sheka: PDP na yiwa Saraki, Tambuwal da Ahmed tanadi na musamman

A daren jiya ne aka tattaro cewa Gwamna Tambuwal na iya sauya sheka bayan an kaa wata kwamiti da zata yanke hukunci akan makomar siyasarsa ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a gobe.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace yawan sauya sheka da jam’iyyar APC mai mulki ta fuskanta kwanan nan baya damun shi ko kadan.

KU KARANTA KUMA: Tsufa na damun ka – Miyetti Allah ga Yakubu Gowon

A cewar wata sanarwa da kakakinsa, Garba Shehu ya saki a ranar Litinin, shugaban kasar yayi Magana a daren ranar Lahadi da yake amsa wata tambaya a lokacin hira da mutanen Najeriya a Togo a ofishin jakadancin Najeriya, Lome.

An tattaro inda Buhari ke cewa shi bai damu da yawan sauya sheka ba saboda yawancin yan Najeriya sun gamsu da kokarin gwamnatinsa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel