Sanatocin da suka sauya sheka masu aikata rashawa ne, kuma suna tsoron a kama su idan Buhari ya sake cin zabe – El-Rufai

Sanatocin da suka sauya sheka masu aikata rashawa ne, kuma suna tsoron a kama su idan Buhari ya sake cin zabe – El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana sanatocin da suka sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress, APC, a matsayin masu rashawa dake tsoron a kada kama su idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lashe zabe a karo na biyu.

Gwamnan yace shugaba Buhari ya tsani cin hanci da rashawa sannan kuma ba zai yi aiki tare da duk dan siyasan dake rashawa don cutar Najeriya ba.

Sanatoci 14 da yan majalisar wakilai 37 ne suka sauya sheka daga APC, ciki harda sanatan Kaduna, Suleiman Hunkuyi, wadda ya koma jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP.

Sanatocin da suka sauya sheka masu aikata rashawa ne, kuma suna tsoron a kama su idan Buhari ya sake cin zabe – El-Rufai

Sanatocin da suka sauya sheka masu aikata rashawa ne, kuma suna tsoron a kama su idan Buhari ya sake cin zabe – El-Rufai

El-Rufai wadda ya bayyana sanatocin da suka sauya sheka a matsayin makiyan shugaba Buhari day an Najeriya ya bayyana hakan ne a yayinda yake amsa tambayoyo a wata hira da harshen hausa wadda akayi a tsahoshin radiya a karshen mako.

KU KARANTA KUMA: Tsufa na damun ka – Miyetti Allah ga Yakubu Gowon

A cewarsa Buhari yayi alkawara uku ga yan Najeriya a lokacin zaben 2019, wadda suka hada da magance rashin tsaro (Boko Haram), habbaka tattalin arzki da kuma yakar cin hanci da rashawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel