Tsufa na damun ka – Miyetti Allah ga Yakubu Gowon

Tsufa na damun ka – Miyetti Allah ga Yakubu Gowon

Kungiyar Miyetti Allah sun bayyana cewa tsufa na damun tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya).

Sakamakon yawan kashe kashe da ake saboda rikicin makiyaya da manoma, Gowon ya bayar da shawarar cewa hukumomin tsaro su gayyaci shugabannin makiyaya domin amsa tambayoyi kan kashe-kashen kasar da rikicin manoma.

Kungiyar sun maida martani ga wannan shawara inda suka bayyana cewa tsufa na damun Gowon, tare da shewa tsohon shugaban kasar na Magana cikin rashin sani.

Tsufa na damun ka – Miyetti Allah ga Yakubu Gowon

Tsufa na damun ka – Miyetti Allah ga Yakubu Gowon

Gowon na da shekaru 83 a duniya yanzu haka.

KU KARANTA KUMA: Sauya sheka daga APC bai damuna ko kadan - Buhari

Gowon ya bayar da wannan shawarar ne a majalisar dokokin jihar Benue, Makurdi, lokacin day a ziyarci gwamna Samuel Ortom don yiwa gwamnati jaje akan kashe-kashen da aka yi da asarar dukiyoyi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel