Da Saraki ya halarci ganawar sanatocin APC da Buhari, da na koreshi daga Aso Villa – Sanata Abdullah

Da Saraki ya halarci ganawar sanatocin APC da Buhari, da na koreshi daga Aso Villa – Sanata Abdullah

Sanata Abdullahi Adamu, sanata mai wakiltan mazabar Nasarawa ta yamma, ya ce da shugaban majalisan dattawa, Bukola Saraki, ya halarci ganawar sanatocin APC da Buhari a makon jiya, da ya fitittikeshi daga fadar shugaban kasa.

Bayan sanatoci 14 na jam’iyyar APC sun sauya sheka, shugaba Buhari ya gayyaci sauran sanatocin da suka rage fadar shugaban kasa amma an nemi shugaban majalisan an rasa.

A wani hira da jaridar Daily Trust, Sanata Adamu Abdullahi ya ce da ya fadawa Saraki “Kai ba dan gidanmu bane; ka yaudari shugaban kasa.”

“Da na yi waje da shi. Da na fada masa shi ba dan gidan nan bane; ka gayyaci shugaban kasa,”

“Kana son ka cigaba da wayon yaudarar ka? Fita daga nan. Babu wani maganar cewa ba zai sauya sheka, bay a APC. Muna fadar shugaban kasa amma bai zo ba. Abinda muka sani shine ya fita.”

Dan majalisan ya kara da cewa shugabannin majalisar dattawa basu da mutunci kuma maciya amana ne.

Da Saraki ya halarci ganawar sanatocin APC da Buhari, da na koreshi daga Aso Villa – Sanata Abdullah

Da Saraki ya halarci ganawar sanatocin APC da Buhari, da na koreshi daga Aso Villa – Sanata Abdullah

KU KARANTA: Dakarun Sojin Najeriya sun bankado wasu tarin Makamai a gidan wani tsagera

"Muna da wani babban matsala na shugabanni maras mutunci, shugabannin da suka fara mulki kan cin amana. Wani irin kallo z aka yiwa wanda aka zaba karkashin wata jam’iyya amma ya kudirta niyya sabawa jam’iyya tun ranan farko?” Yace

Sanata ya ce dukkan wadanda suka sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun yi babban kuskure a rayuwarsu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel