Da dumi-dumi: Yan majalisan dokokin jihar Benue 8 za su tsige gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom

Da dumi-dumi: Yan majalisan dokokin jihar Benue 8 za su tsige gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom

- Za'a tsige gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom

- A makon jiya, jami'an yan sandan Najeriya sun kwace majalisar daga hannun mambobin

- Gwamnan jihar Benue ya sauya sheka daga jam'iyyar da aka zabesa

Takwas daga cikin yan majalisun dokokin jihar Benue talatin sun baiwa gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, sanarwan tsigeshi.

Yan majalisun takwas sun kwace filin majalisar dokokin jihar ne da karfin yan sanda inji mai magana da yawun gwamnan jihar, Tahay Agerzua.

Yace: “Sun kwace majalisar dokokin jihar kuma sun baiwa gwamnan sanarwan tsigeshi duk da cewa akwai umurnin kotun da ya hanasu hakan.”

Mr Agerzua ya ce tsohon gwamnan jihar kuma Sanata mai ci, George Akume ne ya kawo yan sanda daga Abuja domin amfani da su wajen baiwa yan majalisu takwas daman tsige gwamnan.

KU KARANTA: Barayi sun harbe wani dan canji, sun yi awon gaba da kusan miliyan 30

Wannan rikici na faruwa ne bayan gwamnan jihar, Samuel Ortom, ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP.

Kana a kwanakin, yan majalisun PDP 23 da ke majalisan sun tsige kakakin majalisar, Terkimbi Ikyange, kan zargin cewa bay a hada kai da mambobin majalisar wajen gudanar da ayyukan majalisa.

Rahotanni sun bayyana cewa an tsige kakakin, Terkimbi Ikyange, saboda ya ki sauya sheka daga jam’iyyar APC.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel