Yan bindiga sun tafka barna, sun kashe mutane 5 ciki har da Soja guda

Yan bindiga sun tafka barna, sun kashe mutane 5 ciki har da Soja guda

- Matsalar tsaro na cigaba da kwarara sassan kasar nan

- Wasu mahara sun kai wani harin da ya bar gawarwaki biyar ciki har da ta Soja

- Har ya zuwa yanzu ba'a kai ga gano wadanda ke da alhakin harin ba

Ranar Lahadi ta zama abun muni a jihar Akwa-Ibom sakamakon farmaki da wasu ‘yan bindiga suka kaiwa Sojiji a yayin da suke bakin aikinsu wanda hakan ya zama ajalin Soja guda daya da kuma mutane farar hula biyar, sai mutane biyu da suka ji rauni.

Yan bindiga sun tafka barna, sun kashe mutane 5 ciki har da Soja guda

Yan bindiga sun tafka barna, sun kashe mutane 5 ciki har da Soja guda

Jaridar vanguard ta rawaito cewa ‘yan bindigar wanda adadinsu ya kai 50 sun kai farmakin ne da misalin karfe 10:00pm na dare sannan suka farwa sojijin dake gadin dare.

Wani wanda ya ganewa idonsa yayiwa majiyarmu karin haske akan lamarin inda y ace "Yan bindigar sun kama yara biyu sanann suka bi ta cikin dajin da ya hade da hanyar Esop da kuma Iwuekm.

KU KARANTA: Abin tausayi: Barayi sun harbe wani dan canji, sun yi awon gaba da kusan miliyan 30

"Jim kadan bayan dauke yaran suna cikin tafiya ne suka bullo ta daidai shataletalen da zai kai ga titin asibiti wanda a nan suka yi arba da jami'an sojin".

"Da yake sojin basa cikin shirin ko zata kwana, gasu da yawan gaske, nan take suka bude musu wuta suka kashe soja daya tare da kone motar jami'an Sojin".

Wata majiya ta bayyana cewa mutane biyu da suka rasa rayukansu sun fito ne daga kauyen Ika da kuma Ukanafun.

Sai kuma ragowar ukun da suka fita daga kauyen Iwukem a yayin da al'amarin yake faruwa".

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Madcon Ogbechie ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace yanzu haka suna cigaba da bincike.

Shi ma daga bangarensa wani jami'in dan sanda daga yankin Etim Ekpo yace wannan ba shi da nasaba da irin masu yin asiri da sannan jikin dan Adam ba, inda ya sake kira ga jama'a wajen ganin sun bada hadin kai domin kawo karshen irin wadannan tashin hankali.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel