Kwankwaso ya kaiwa Fani-Kayode ziyara ta musamman

Kwankwaso ya kaiwa Fani-Kayode ziyara ta musamman

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma sanata mai wakiltan mazabar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya kaiwa babban dan adawan shugaba Buhari kuma tsohon ministan sufurin jirgin sama, Femi Fani-Kayode, ziyara.

Kwankwaso ya hadu da Fani Kayode a jiya, 29 ga watan Yuli, 2018 ne a gidan tsohon ministan da ke babban birnin tarayya Abuja.

Legit.ng ta samu wannan rahoto ne daga bakin Fani-Kayode inda ya ce: “ Cikin karamci da kuma mutunci ni da Precious muka karbi bakunin abokina kuma dan uwana, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso, a gidanmu dake Abuja da ranan nan."

Mun tattauna kan abubuwan da suka shafin kasa da kuma yadda za mu fuskanci gobe. Kwankwassiya!!!”

Kwankwaso ya kaiwa Fani-Kayode ziyara ta musamman

Kwankwaso ya kaiwa Fani-Kayode ziyara ta musamman

Sanata Kwankwaso ya yi wannan ganawar ne bayan haduwa da shahrarren abokin hamayyarsa, Malam Ibrahim Shekarau, kan yadda za su hada kai wajen tabbatar da cewa sun samu nasara a zabe 2019.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya isa kasar Togo domin halartan taron ECOWAS/ECCAS

Bayan ganawar, Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa shi da Sanata Kwankwaso ne jagororin jam’iyyar PDP a jihar Kano.

Kwankwaso dai ya fara wadannan ziyarce-ziyarce ne bayan sauya sheka da yayi daga jam’iyyar APC zuwa PDP a ranan Talata, 24 ga watan Yuli, 2018.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel