Abin tausayi: Barayi sun harbe wani dan canji, sun yi awon gaba da kusan miliyan 30

Abin tausayi: Barayi sun harbe wani dan canji, sun yi awon gaba da kusan miliyan 30

- Wasu da kyautata cewa 'yan fashi ne sun hallaka wani dan canji bayan kwace masa makudan kudade

- Sun biyo shi ne tun da ya fito daga gida har zuwa lokacin da ya karbo su

- Bayan kwatar kudin ne sai suka kuma harbe shi a kirji wanda hakan yayi ajalinsa

Rundunar 'yan sanda ta kasa reshen jihar Lagas suna gudanar da bincike akan kisan wani mai sana'ar canjin kudi mai suna Victor Thorpe da wasu mutane su ka kashe sannan suka arcewa da kudinsa sama da Naira miliyan 28.

Abin tausayi: Barayi sun harbe wani dan canji, sun yi awon gaba da kusan miliyan 30

Abin tausayi: Barayi sun harbe wani dan canji, sun yi awon gaba da kusan miliyan 30

Lamarin ya faru ne a ranar Juma'a a lokacin da dan canjin ya je zuwa ga kamfaninsa wanda yake kan titin Ahmadu Bello, a unguwar Victoria Island, domin daukar wasu kudade..

Jim kadan da dakko wadannan makudan kudaden ne, sai wasu mutane akan Babur suka sha gaban motar hayar da yake ciki, inda dayan ya warce jakar dake hannunsa yayin da dayan kuma ya harbe shi a kirji.

KU KARANTA: Fusatattun matasa sun kai farmaki ofishin yan sanda a jihar Zamfara

Wata Majiya ta bayyana cewa "Victor, ya ajiye motarsa ne, sannan ya shiga motar haya saboda gudun haduwa da barayi, ashe barayin suna lura da shi tun lokacin da ya fito domin zuwa daukar kudaden".

Kai tsaye suka bukaci da ya bayar da kudin, bayan ya bayar da kudin ne, sai suka harbe shi a kirjinsa, duk da cewa akwai sauran mutane a cikin motar amma shi kadai aka kaiwa wannan harin".

"Mutumin kirki kuma mai bin tafarkin addinin kirista yadda ya kamata, ya mutu ya bar kanana yara domin kuwa babban dan sa shi ne mai kimanin shekaru 15" in ji majiyar.

Bayan an harbe shi, sai aka garzaya da shi zuwa asibitin Sojoji dake kan titin Awolowo domin ceton ransa.

Kakakin rundunar yan sanda ta jihar Chike Oti Legas ya bayyana cewa an samu nasarar cafke wasu mutane guda 7 da ake zargin suna da alaka da kisan dan canjin.

Kawo yanzu dai an mayar da lamarin zuwa ofishin ‘yan sanda da ke Ikeja domin zurfafa bincike.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel