Mahara sun so kashe ni ne – Sanata Dino Melaye

Mahara sun so kashe ni ne – Sanata Dino Melaye

Dan majalisa mai wakiltan mazabar Kogi ta yamma a majalisar dattawa, Sanata Dino Melaye ya ce sabanin rahotannin garkuwa da shi, yan bindigan da suka kaiwa motarshi hari a hanyarsa na zuwa jiharKogi a ranar Alhamis sun so kashe shi ne.

Melaye wadda yayi jawabi ga yan jarida a Abuja a ranar Lahadi, yace ya tserema yunkurin kashe shi a kewayen Gwagwalada hanyar Abuja zuwa Lokoja a hanyarsa na zuwa shari’an kotu a Lokoja, babban birnin jihar.

Melaye yace ya ruga da gudu cikin daji sannan ya boye a kan bishiya na tsawon sa’o’i 11.

Mahara sun so kashe ni ne – Sanata Dino Melaye

Mahara sun so kashe ni ne – Sanata Dino Melaye

Dan majalisan yayi bayanin cewa ya bar Abuja da safiyar ranar Alhamis don tafiya Lokoja sannan ya lura cewa wata motar Toyota Sienna na bibiyar shi. Yace sai motar ta sha gaban motarsa, suka kare masa hanya sannan mutanen cikin motar suka fara harbin motarsa.

KU KARANTA KUMA: Abun dariya ne APC bata so Dogara ya bar jam’iyyar – Yan majalisar wakilai

Dan majalisan, wadda ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP a ranar Talata, yace lokacin da makisan suka gano cewa motarsa ba mai jin harbi bane, sai suka yi kokarin kona ta.

Yace da ya ga haka sai ya bude motar ya fada daji da gudu, sannan sai ya dare kan bishiya. A lokacn da yake kan bishiya sai ya ga jami’an yan sanda biyu dake nemansa amma basu san yana saman bishiya ba, ya kara da cewa sai da ya shafe sa’o’i 11 a saman bishiyan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel