Kakar sauyin sheka: Sanatoci 7 sun kammala shirin komawa jam'iyyar APC daga PDP

Kakar sauyin sheka: Sanatoci 7 sun kammala shirin komawa jam'iyyar APC daga PDP

Jagora a zauren majalisar dattijan Najeriya, Sanata Mohammed Ali Ndume dake wakiltar mazabar jihar Borno ta kudu a jam'iyyar APC yace kawo yanzu dai akalla 'yan majalisar ta su bakwai ne daga PDP suka kammala shire-shiren su na komawa APC.

Ndume, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yaje fira da wakilin majiyar mu yace iya kwarewa a fagen siyasa ne ya sanya har yanzu jam'iyyar ta APC ke da rinjaye.

Kakar sauyin sheka: Sanatoci 7 sun kammala shirin komawa jam'iyyar APC daga PDP

Kakar sauyin sheka: Sanatoci 7 sun kammala shirin komawa jam'iyyar APC daga PDP

KU KARANTA: An nada sabon kwamandan rundunar Lafiya Dole

Legit.ng ta samu cewa Sanata Ndume ya kara da cewa sauyin shekar da aka samu a zauren majalisar a satin da ya gabata ya koya masu hankali inda yanzu suka kara zama tsintsiya madaurin ki daya.

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Nasarawa dake a yankin Arewa ta tsakiya watau Umar Tanko Al-makura ya sauke kwamishinonin sa tara da kuma masu bashi shawara biyu daga mukaman su a karshen satin da ya gabata.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar da Sakataren gwamnatin jihar Mohammed Abdullahi ya fitar dauke da sa hannun sa a garin Lafiya, babban birnin jihar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel