Mafusatan matasa sun lakadawa 'yan APC din da suka canza sheka dukan tsiya

Mafusatan matasa sun lakadawa 'yan APC din da suka canza sheka dukan tsiya

Wasu gungun mafusatan matasa da ake zargin hayar su aka dauka sun yi wa wasu 'yan siyasar da suka canza sheka daga jam'iyyar APC mai mulki zuwa ADP dukan tsiya a garin Osogbo na jihar Osun.

Majiyar mu ta ruwaito cewa a yayin artabun, tsohon shugaban karamar hukumar Oriade mai suna Taiwo Fatiregun da wasu mutane hudu sun samu raunuka da dama.

Mafusatan matasa sun lakadawa 'yan APC din da suka canza sheka dukan tsiya

Mafusatan matasa sun lakadawa 'yan APC din da suka canza sheka dukan tsiya

KU KARANTA: Sunayen mutane 45 da ke harin kujerar Buhari a 2019

Legit.ng ta samu cewa Mista Taiwo ya kara da cewa suna cikin taron su na siyasa ne a karamar hukumar Ijebu Jesa kawai sai suka ji saukar duka daga matasan.

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Nasarawa dake a yankin Arewa ta tsakiya watau Umar Tanko Al-makura ya sauke kwamishinonin sa tara da kuma masu bashi shawara biyu daga mukaman su a karshen satin da ya gabata.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar da Sakataren gwamnatin jihar Mohammed Abdullahi ya fitar dauke da sa hannun sa a garin Lafiya, babban birnin jihar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel