Wani gwamna a Arewa yayiwa kwamishinonin sa 9 kakkabar 'ya'yan kadanya

Wani gwamna a Arewa yayiwa kwamishinonin sa 9 kakkabar 'ya'yan kadanya

Gwamnan jihar Nasarawa dake a yankin Arewa ta tsakiya watau Umar Tanko Al-makura ya sauke kwamishinonin sa tara da kuma masu bashi shawara biyu daga mukaman su a karshen satin da ya gabata.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar da Sakataren gwamnatin jihar Mohammed Abdullahi ya fitar dauke da sa hannun sa a garin Lafiya, babban birnin jihar.

Wani gwamna a Arewa yayiwa kwamishinonin sa 9 kakkabar 'ya'yan kadanya

Wani gwamna a Arewa yayiwa kwamishinonin sa 9 kakkabar 'ya'yan kadanya

KU KARANTA: Kuzo kuga hotunan gidan da yafi kowane tsada a Najeriya

Legit.ng ta bayyana cewa gwamnan ya dauki wannan matakin ne domin ya baiwa wadanda aka sauke din damar cigaba da harkokin su na siyasa.

A wani labarin kuma, Wasu gungun mafusatan matasa da ake zargin hayar su aka dauka sun yi wa wasu 'yan siyasar da suka canza sheka daga jam'iyyar APC mai mulki zuwa ADP dukan tsiya a garin Osogbo na jihar Osun.

Majiyar mu ta ruwaito cewa a yayin artabun, tsohon shugaban karamar hukumar Oriade mai suna Taiwo Fatiregun da wasu mutane hudu sun samu raunuka da dama.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel