Kaico! Ambaliyan ruwa ya ci mutane 5 yan gida daya a jihar Jigawa

Kaico! Ambaliyan ruwa ya ci mutane 5 yan gida daya a jihar Jigawa

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya sauka a karamar hukumar Babura ya yi sanadin mutuwar mutane shidda a cikin kwanaki uku da suka gabata, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta bayyana cewa mutanen su shida sun gamu da ajalinsu ne bayan an sha ruwa na sama da awanni biyu a garin, wanda yayi sanadin mutuwar mutane biyar daga cikinsu yan gida daya, nan take.

KU KARANTA: Nahiyar Turai ta baiwa El-Rufai tallafin naira biliyan 4.2 don kammala wani muhimmin aiki

Yan gida dayan sun mutu ne sakamakon faduwar katangar dakinsu dake kofar Yamma, wanda ya sanya rufin dakin gaba daya ruftawa akansu, yayin da mamacin na shidda ya rasu a babban Asibiti Babura yayin jinyar karayar da ya samu a kafa.

A nasa bangaren, shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jihar, Yusuf Sani, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana sunayen mamatan kamar haka; Saro Habu, Maryam Habu, Bilk Habu, Hafsa Habu da Usman Habu.

Idan za’a tuna an samu ambaliyar ruwa a damInar bana a jihohi da daman a yankin Arewa, musamman jihohin Katsina, Bauchi, Yobe da Jigawa, wanda hakan yayi sanadin asarar rayuka da dukiya da dama.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel