Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane 15 a jihar Zamfara – Kaakakin Majalisa

Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane 15 a jihar Zamfara – Kaakakin Majalisa

Kaakakin majalisar jihar Zamfara, Sanusi Rakiji ya bayyana cewa wasu yan bindiga da suka addabi al’ummar jihar sun yi garkuwa da mutane goma sha biyar a karamar hukumar Maradun, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Rakiji ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, 29 ga watan Yuli a garin Gusau, inda yace ana bukatar garambawul da tsarin harkar tsaro a jihar Zamfara.

KU KARANTA: Dakarun Sojin Najeriya sun bankado wasu tarin Makamai a gidan wani tsagera

Rakiji ya koka tare da nuna bacin ransa game da yadda yan bindiga suka kama kayuka goma sha takwas dake cikin karamar hukumar Zurmi, wanda yace wannan hari ya tabbatar da tabarbarewar tsaro a jihar, tare da bukatar daukar matakan gaggawa.

“Ya kamata jami’an tsaro su tashi tsaye, domin a gaskiya muna bukatar matakan tsaki na dindindin, duk da haka muna gode da irin rawar da gwamnatin tarayya ke takawa game da lamarin, don a yanzu haka ta turo da karin Sojoji zuwa yankunan da abin ya shafa.

“Zuwa yanzu an samu kwanciyar hankula a yankin, don haka muke kira ga al’ummar yankin da su zauna lafiya da junansu.” Inji shi.

Daga karshe Kaakakin ya yaba ma Sarkin kasar Zurmi, Alhaji Abubakr Atiku sakamakon yadda ya nuna damuwarsa da halin da jama’ansa ke ciki, sa’annan ya jinjina masa bisa kokarin karesu da yake yi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel