Dakarun Sojin Najeriya sun bankado wasu tarin Makamai a gidan wani tsagera

Dakarun Sojin Najeriya sun bankado wasu tarin Makamai a gidan wani tsagera

Dakarun rundunar Sojan kasa na Najeriya sun bankado wasu tarin muggan makamai da suka hada da bindigu da alburusai akan hanyar Agbura zuwa Otuoke dake cikin karamar hukumar Ogbia na jihar Bayelsa, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sojojin sun yi wannan kame ne a yayin wani samame da suka kai a ranar lahadi, 29 ga watan Yuli, inda suka gano bindigun AK 47 guda hudu, sai kuma bindiga kirar G3 guda biyu itama.

KU KARANTA: Wata Kotu ta tasa keyar yan fashi da makami guda 3 dake fakewa da sana’ar Achaba

Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewar Sojojin sun sake gano wadansu makamai a gidan wani fitaccen tsagera daga cikin tsagerun Neja Delta mai suna Emmanuel Lawanson, inda anan ma sun gano kananan bindiga kirar Berreta guda biyu,kayan sawan Soji da alburusai da dama.

Bugu da kari a yayin samamen, Sojojin sun yi nasarar cafke wani na abokin tabargarzar Lawanson, mai suna Ebikabore Emmanuel, kamar yadda kaakakin rundunar Sojin kasa, Texas Chukwu ya bayyana.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel