Malamin addinin da ya sace Manjo a hukumar soji ya shiga hannu

Malamin addinin da ya sace Manjo a hukumar soji ya shiga hannu

Wani malamin addinin Kirista mai rike da mukamin mataimakin Fasto a wata Coci (Favour Minsitry) dake garin Ugbiyokho a karamar hukumar Egor ta jihar Delta ya shiga hannu bisa zarginsa da sace Manjo Stephen Omoigui (mai ritaya) tare da wata yarinyar shagonsa.

An sace Manjo Omogui tare da yarin dake masa aiki a ranar 6 ga watan Yuni a garin Iguosa dake kan hanyar Benin zuwa Legsa a jihar Edo.

An sake su bayan an biya masu garkuwa das u kudin fansa.

Mutumin day a sace tsohon sojan, Fasto Okafor, ya bayyana cewar ya shiga sana’ar sace mutane ne saboda samun kudin da zai dauki dawainiyar jinyar mahaifinsa dake fama da matsalar ido.

Malamin addinin da ya sace Manjo a hukumar soji ya shiga hannu

Malamin addinin da ya sace Manjo a hukumar soji ya shiga hannu

Da yake Magana da manema labara yayin da aka yi bajakolinsu tare da wasu gungun masu laifi, Fasto Okafor ya bayyana cewar wani mai suna Mathew da suka hadu a gidan yari ne ya shigar da shi cikin wannan muguwar dabi’a.

DUBA WANNAN: Ga koshi ga kwanan yunwa: Yadda wahalar manoman Najeriya ke tafiya a banza

Fasto Okafor ya kara da cewa, “wata rana ina Mathew ya kira ni tare da sanar da ni cewar mu hadu a gidan wani gidan man fetur dake Ring Road. Bayan na same su ne suka ce min na shigo mota mu je a sato wani mutum. Na so nayi masu musu amma ganin bindigu a hannunsu sai nayi shiru.

Sai dai Okafor ya ce bay a cikin wadanda ke karbo kudin fansa idan sun sace mutum kuma ba a taba ba shi ko sisi ba har ya zuwa lokacin da jami’an ‘yan sanda suka kama shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel