Rashin imani: ‘Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace mai-jego da 'yarta

Rashin imani: ‘Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace mai-jego da 'yarta

- 'Yan bindiga sun sake tafka wata babbar katobara a Kaduna

- Sun kashe mutane 3 sun sace wata mata mai shayarwa da 'yarta

- Mutanen garin sun yi kira ga gwamnati da a kai musu dauki don kawo karshen matsalar

Rahotanni daga yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna sun bayyana cewa ‘yan bindiga sun kashe a kalla mutane uku tare da awon gaba da mutane bakwai, daga ciki har da masu shayarwa guda biyu da kuma jaririya yar kwanaki takwas da haihuwa.

Rashin imani: ‘Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace mai-jego da danta

Rashin imani: ‘Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace mai-jego da danta

Kamar yadda shugaban ‘yan kwamitin tsaro da sa ido a yankin Ibrahim Nagwari ya bayyana, ya ce lamarin ya faru ne a yankin ‘Dan-baki dake kauyen Sabon Layi da misalin karfe 7:00pm na dare.

Ya ce akwai matar da aka yi garkuwa da ita tare da jaririyarta ‘yar kwanaki takwas da haihuwa, sannan ‘yan bindigar sun yi awon gaba da wasu shanun mutanen yankin.

KU KARANTA: Abin tausayi: Barayi sun harbe wani dan canji, sun yi awon gaba da kusan miliyan 30

Garba Tanko wanda yana daya daga cikin wanda ya ganewa idonsa yadda abin ya faru ya ce "Al'amarin ya faru daidai lokacin sallar magriba. Sun yi gaba da wasu shanu wanda muke yin amfani da su wajen noma a gonakinmu".

"Yan bindigar suna amfani ne da dajin Kumaku da Kuyambana wajen tada hankalin manona a yankin nan".

"Duk da cewar akwai Sojoji da jami'an ‘yan sanda musamman akan titin zuwa Birnin Gwari da hanyar zuwa Funtua, amma duk da haka muna kira ga gwamnatin tarayya da ta karo jami'an tsaro domin kawo karshen masu yin garkuwa da mutane a yankin na Birnin Gwari". Tanko ya shaida.

Har ya zuwa lokacin hada rahotan nan dai majiyarmu ta gaza samun Muktar Aliyu wanda shi ne mai magana da yawun hukumar ‘yan sanda ta jihar Kaduna a waya domin jin ta bakinsa game da wannan lamarin.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel