Gwamnatin tarayya ta bawa yaran Saraki umarnin ajiye mukamansu ko a tsige su

Gwamnatin tarayya ta bawa yaran Saraki umarnin ajiye mukamansu ko a tsige su

Gwamnatin tarayya ta umarci dukkan yaran shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, dake rike da mukaman siyasa su ajiye aiki aiyukansu da gaggawa ko kuma ta tsige su.

A cikin satin da muka yi bankwana da shi ne, 6 daga cikin ‘yan majalisar wakilai daga jihar Kwara suka canja sheka, tare da ragowar wasu mambobin majalisar 31, zuwa jam’iyyar PDP.

Da yake bayar da wannan sanarwar yau, Lahadi, a garinsa na haihuwa, Oro, dake karamar hukumar Irepodun ta Kwara, ministan al’adu da yada labarai, Lai Mohammed, ya bayyana cewar gwamnatin tarayya zata rushe zaben shugabannin jam’iyyar APC na jihar tare da sake wani sabo.

Gwamnatin tarayya ta bawa yaran Saraki umarnin ajiye mukamansu ko a tsige su

Bukola Saraki

Saraki ne ya kafa dukkan shugabannin jam’iyyar APC a jihar Kwara karkashi yaronsa, Alhaji Ishola Balogun Fulani, kuma jam’iyyar APC ta kasa karkashin sabon shugabanta Adams Oshiomhole ta karbe su a matsayin shugabannin APC a jihar ta Kwara.

Lai Mohammed ya bayyana cewar daukar wannan mataki ya biyo bayan tuntuba da masu ruwa da tsaki suka yi tsakanin ranakun Juma’a da Asabar.

DUBA WANNAN: Masu garkuwa sun dawo da dan hadimin gwamnan Katsina da wata wasika a aljihunsa, duba hotuna

Ministan ya sanar da cewar za a sake sabon zaben shugabannin mazabu, kananan hukumomi da kuma matakin jiha.

Dangane da batun sauke yaran Saraki masu rike da mukamai a gwamnatin tarayya, Lai Mohammed ya bayyana cewar ba zata yiwu wasu ‘ya’yan jam’iyyar na zaune babu mukami ba amma wadanda suka fita na cigaba da rike mukamai a gwamnati.

Lai ya kara da cewa idan basu ajiye mukamansu bayan samun wannan sanarwa ba, to gwamnati zata tsige su domin babu amfanin cigaba da zama da mutanen zasu ke yiwa gwamnati makarkashiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel