Mutane sun kai kuka wajen Shugaban kasa game da kashe-kashen Zamfara

Mutane sun kai kuka wajen Shugaban kasa game da kashe-kashen Zamfara

Yanzu haka da mu ke magana, mutane da dama sun fito sun koka da yadda ake kashe al’umma a Jihar Zamfara. Wani Bawan Allah daga Jihar Zamfara ya koka da irin ta’asar da ake yi a Yankin.

Mutane sun kai kuka wajen Shugaban kasa game da kashe-kashen Zamfara

An kai kuka wajen Buhari game da kashe-kashe

Musab Isah Mafara yayi amfani da shafin sa na Facebook inda yayi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kawo karshen irin kisan da ake yi wa al’umma ba su ji ba kuma ba su gani ba. Abin dai yayi mahaukacin kamari a halin yanzu.

KU KARANTA: Dakarun Soji sun kashe 16 tare da kwato motocin yaki da bindigu

Wannan Bawan Allah dai ya nemi Gwamnatin Tarayya ta kawo masu dauki a daina hallaka al’umma. Musab Marafa yace ba nema su ke yi a gina masu jirgin kasa ba kamar yadda aka yi wa sauran Jihohi ba illa kurum a kare ran mutanen Garin.

Mutanen Zamfara dai ba nema su ke yi a kawo masu tituna da gina Makarantu ba, sai dai kurum su na nema ne a martaba rayukan jama’a. Kwanakin baya dai aka kashe mutane sama da mutane 20 yayin da su ke sallah a wani Gari a cikin Zamfara.

Kun ji labari dazu cewa Air Marshal Abubakar watau Shugaban Hafsun Sojin na sama ya bayyana cewa sun horas da Sojoji sama da 2000 wanda yanzu an tura wasu Jami’an Sojojin zuwa Yankin Zamfara da ake rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel