Gwamnan Bauchi ya taimakawa Sojojin Najeriya wajen kawo tsaro da zaman lafiya

Gwamnan Bauchi ya taimakawa Sojojin Najeriya wajen kawo tsaro da zaman lafiya

A cikin kokarin da Gwamnatin Jihar Bauchi ta ke yi na inganta karfin Rundunar Sojin sama na kasar nan, mun samu labari cewa Gwamna Mohammed Abubakar ya Sojojin kasar kayan aiki da dama.

Gwamnan Bauchi ya taimakawa Sojojin Najeriya wajen kawo tsaro da zaman lafiya

Gwamnatin Bauchi ta taimakawa Sojojin sama na Najeriya

Kamar yadda mu ke samun labari daga gidan Soja, Gwamnan Bauchi Mohammed Abubakar ya rabawa Sojoji manyan motoci ga Jami’an da ke aiki a Lame da Garin Bura a Jihar. Gwamnan ne ya bayyana wannan a jiya Asabar.

Sojojin saman na Najeriya sun bude wani wuri na mussaman ne na koyon aiki inda za a rika daukar horo wajen harbi da sauran su. Bayan wannan Rundunar Sojin saman ta bude gidajen manyan Jami’an ta a cikon Garin Bauchi.

KU KARANTA: Sojojin kasa na Najeriya sun kashe wasu 'Yan Boko Haram

Gwamna Mohammed Abubakar shi ne babban bako wajen taron da aka yin a kaddamar da wannan ayyuka. Gwamnan ya yabawa kokarin da Sojojin kasar musamman Shugaban Hafsun Sojin sama yake yi na kawo gyara a gidan Sojin.

Air Marshal Abubakar wanda asalin ‘Dan Jihar Bauchi ne kuma shi ne Shugaban Hafsun Sojin na sama ya bayyana cewa sun horas da Sojoji sama da 2000. Yanzu an tura wasu Jami’an Sojojin zuwa Yankin Zamfara da ake rikici.

Olatokunbo Adesanya wanda shi ne babban Jami’in yada labarai na gidan Sojan ya bayyana mana wannan a shafukan sada zumunta. Operation Sharan Daji na cigaba da aiki domin maganin tsageru.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel