Masu garkuwa sun dawo da wani dan hadimin gwamnan Katsina, duba wasikar da suka hado shi da ita

Masu garkuwa sun dawo da wani dan hadimin gwamnan Katsina, duba wasikar da suka hado shi da ita

A jiya, Asabar, ne wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace wani yaro mai suna Jafar, da ga Alhaji Sabo, mai taimakawa gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, a kan raya aiyuka.

Saidai a wani yanayi kamar a na shirin wasan kwaikwayo, an sako yaron daga baya tare das aka wata wasika a cikin aljihunsa dake kira ga gwamnatin jihar da ta samar da aiyuka ga matasa.

Masu garkuwa sun ce, sun sace yaron ne domin neman miliyan N10m a matsayin kudin fansa amma sai daga imani ya zo masu suka saki yaron haka siddan.

Masu garkuwa sun dawo da wani dan hadimin gwamnan Katsina, duba wasikar da suka hado shi da ita

Yaro Jafar da aka sace

A cikin wasikar ta su, sun bayyana yadda suka bawa yaron wasu kwayoyin bacci da suka dauke masa hankali amma daga baya tsoron Allah ya saka su canja niyyar su.

Kazalika sun shawarci mahaifiyar yaron da ta kula da yaron sosai saboda a cewar su, mutumin kirki ne.

DUBA WANNAN: Dakarun soji sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram 16 tare da kwato muggan makamai da motocin yaki bayan wani artabu mai yaji (Hotuna)

Wani dan uwa ga yaron da aka sace ya shaidawa manema labara cewar yanzu haka yaron na samun kulawar masana harkar lafiya yayin da ‘yan sanda suka fara binciken lamarin.

Masu garkuwa sun dawo da wani dan hadimin gwamnan Katsina, duba wasikar da suka hado shi da ita

Wasikar da suka hado shi da ita

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel