Fusatattun matasa sun kai farmaki ofishin yan sanda a jihar Zamfara

Fusatattun matasa sun kai farmaki ofishin yan sanda a jihar Zamfara

- Kashe-kashen da ake yawaita yi a jihar Zamfara ya fusata samarin jihar

- Har sunyi yunkurin kwato su a hannun jam'ian 'yan sanda

- Bayan artabu 'yan sanda sun tseratar da masu laifin da ake zargin da hannunsu a ciki hare-haren da ake kaiwa jihar

Wasu fusatattun matasa a garin Zurmi, dake karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara sun kai farmaki ofishin ‘yan sanda da nufin lallai sai jami'an ‘yan sandan sun danka musu mutane ukun da aka kama bisa zargin kai hare-hare jihar.

Fusatattun matasa sun kai farmaki ofishin yan sanda a jihar Zamfara

Fusatattun matasa sun kai farmaki ofishin yan sanda a jihar Zamfara

Kakakin hukumar ‘yan sanda na jihar SP Muhammadu Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace matasan sun kawo wannan farmaki ne ranar lahadi da yamma.

Shehu ya ce matasan wadanda suke cikin bacin rai sun kona mota da babura a ofishin, sannan ya tabbatar da cewa mutane ukun da aka kama suna da hannu a harin da aka kai a ranar 24 ga watan Yuli a kauyen Mashema.

Kakakin ‘yan sandan ya shaida cewa jim kadan bayan sanar da nasarar cafke mutane ukun wadanda ake zargin suna da hannu a cikin wancan hari da aka kai, sai wasu matasan yankin suka hadu tare da zuwa ofishin ‘yan sandan.

KU KARANTA: Boko Haram: Dakarun Soji sun kashe 16 tare da kwato motocin yaki da bindigu, duba hotuna

Amma matasan basu cimma burinsu na kwatar masu laifin ba domin daukar doka a hannu ba, saboda jami'an yan sandan wannan ofishi sun yi nasarar dauke masu laifin daga wannan ofishin kafin abubuwa suyi tsamari.

Ya kara da cewa ya zuwa yanzu komai ya dawo daidai, kuma masu laifin an damka su ga babbar shelkwatar ‘yan sandan jihar domin cigaba da bincikarsu.

Hukumar ‘yan sanda ta jihar ta yi kira ga jama'ar jihar da su zama masu bin doka da oda da kuma gujewa daukar doka a hannunsu.

Kamfanin dillancin labarai ya rawaito cewa ‘yan gudun hijira sama da 12,000 ne daga kauyuka 18 dake karamar hukumar ta Zurmi suke cigaba da karbar kulawa a wani kebantacce wuri da gwamnatin jihar ta ware a karamar hukumar ta Zurmi.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel