Na fi Buhari cancanta don na fi shi ilimi - Dan takarar shugaban kasa a PDP

Na fi Buhari cancanta don na fi shi ilimi - Dan takarar shugaban kasa a PDP

Kabiru Tanimu Turaki na daya daga cikin masu neman jam'iyyar PDP ta tsayar da su takarar shugaban kasa a zaben 2019, ya ce ya fi Buhari cancanta da mulkin Najeriya saboda gaba yake da shi ta fuskar ilimi.

Turaki, babban lauya ne mai lambar SAN, sannan ya ce ya fi Buhari cancanta ne saboda ya fi shi ilimin boko da kuma na shari'a.

Tsohon minista a lokacin mulkin jam'iyyar PDP karkashin Goodluck Jonathan, Tanimu Turaki na daga cikin mutane 7 da ya zuwa yanzu suka bayyana sha'awar takarar shugaban kasa domin gwabzawa da shugaba Buhari a 2019.

Na fi Buhari cancanta don na fi shi ilimi - Dan takarar shugaban kasa a PDP

Dan takarar shugaban kasa a PDP; Tanimu Turaki

Tanimu Turaki dan asalin jihar Kebbi ne kuma daya cikin wadanda suka zauna a PDP duk da rikicin shugabanci da tayi ta fama da shi.

Turaki ya bayyana cewar akwai fahimtar juna tsakanin 'yan takarar jam'iyyar ta PDP, a saboda haka ya ce ba za a fuskanci kowacce matsala ba duk wanda a karshe ya samu nasarar a zaben fitar da dan takara.

A shekarar 2015 ne jam'iyyar APC ta kayar da gwamnatin PDP bayan ta shafe shekaru 16 tana mulkin Najeriya.

DUBA WANNAN: 2019: Shugaba Buhari ya bukaci a dakatar da yakin neman zabensa

Jam'iyyar PDP na saka ran sake komawa kan karagar mulkin Najeriya a zaben shekarar 2019 mai zuwa.

'Yan jam'iyyar APC mai mulki na cigaba tsallakawa zuwa jam'iyyar PDP, wani lamari dake karawa jam'iyyar ta PDP karfin gwuiwar ganin cewar zata iya samun nasara a zaben na shekarar 2019.

Ko a satin da ya kare saida mambobin majalisar dattijai 15 da na majalisar wakilai 37 suka canja sheka daga APC zuwa PDP kafin daga bisani gwamna Ortom na jihar Benuwe ya fice daga jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel