Wani ‘Dan Majalisa a Jihar Oyo ya fice daga APC ya koma APC

Wani ‘Dan Majalisa a Jihar Oyo ya fice daga APC ya koma APC

A cikin makon da ya gabata ne wani ‘Dan Majalisar dokokin Jihar Oyo da ke wakiltar Ibadan watau Hon. Olusegun Olaleye ya fice daga Jam’iyyar APC mai mulki ya dawo Jam’iyyar adawa watau PDP.

Wani ‘Dan Majalisa a Jihar Oyo ya fice daga APC ya koma APC

Jam'iyyar APC ta sake yin wasu asara a Majalisun Najeriya
Source: Depositphotos

‘Dan Majalisar da ke wakiltar Arewacin Ibadan ya sauya shekan ne a Ranar Alhamis inda ya samu kyakkayawar tarba daga Shugaban Jam’iyyar PDP na Yankin watau Seun Adelore. APC dai na kara rasa jama’a a Jihar Oyo.

Olusegun Olaleye ya fice ne daga APC bayan ganin wasu ‘Yan Majalisar Tarayya sun yi watsi da Jam’iyyar da ke mulki. ‘Dan Majalisar Jihar ya soki APC saboda kauce hanya da tayi wanda yace shiyasa ya koma PDP.

KU KARANTA: An tona asirin wani dan takarar Gwamnan PDP maras takardun karatu

Yanzu dai Jam’iyyar PDP tana kara karfi a Jihar inda ta ke da manya irin su tsohon Gwamna Rashidi Ladoja, da Sarafadeen Alli da kuma Sanata Femi Lanlehin. Shugaban PDP ya tabbatar da cewa sun shiryawa zaben 2019.

Kwanan ne kuma wani ‘Dan Majalisan APC a Bauchi ya bar Jam’iyyar inda ya koka da rashin adalci. Aminu Tukur ya zargi Jam’iyyar da kin cika alkawarin da ta dauka wajen shirya zaben fitar da gwani na kujerar Sanata a Jihar.

Idan ba ku manta ba kwanaki kun ji cewa ‘Yan Tawaren da ke Jam’iyyar APC da ke karkashin Unity Forum a Oyo da ke Kudu maso Yammacin Najeriya sun tattara kayan su sun koma Jam’iyyar adawa ta ADC da ke kokarin tasowa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel