2019: Wani tsohon na-kusa da Obasanjo da Jonathan yace tsakanin Buhari da Saraki za a gwabza

2019: Wani tsohon na-kusa da Obasanjo da Jonathan yace tsakanin Buhari da Saraki za a gwabza

Labari ya iso gare mu cewa wani tsohon Hadimin Goodluck Jonathan da kuma Olusegun Obasanjo a lokacin su na shugabannin kasa watau Dr. Doyin Okupe yayi magana game da yadda za buga a zaben 2019.

2019: Wani tsohon na-kusa da Obasanjo da Jonathan yace tsakanin Buhari da Saraki za a gwabza

Kujerar Saraki na nan ko ya bar APC - Doyin Okupe

Dr. Doyin Okupe yace a zaben mai zuwa na 2019 tsakanin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki za a gwabza. Okupe ya bayyana wannan ne a gidan Talabijin jiya Asabar.

Babban ‘Dan siyasar ya tattauna ne game da sauya shekar da wasu ‘Yan Majalisa su kayi daga Jam’iyyar APC zuwa PDP. Doyin Okupe yace idan har Bukola Saraki yana da wayau ya kamata ya nemi takarar Shugaban kasa.

KU KARANTA: 'Yan wasan Hausa sun ba Gwamna Ganduje lambar yabo

Dr. Okupe ya nuna cewa Bukola Saraki ne ‘Dan siyasar da ya fi kowa karfi a kasar nan bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari a halin yanzu. Okupe ya kuma ce zai yi kyau Saraki ya fice daga APC ya jarraba farin janin sa a kasar.

Tsohon mai ba Shugabannin kasar nan shawaran yace babu dalilin da zai sa Saraki ya cigaba da zama a Jam’iyyar APC ganin irin yadda Gwamnati ta muzguna masa ya kuma ce Saraki ba zai rasa mukamin sa ba a Majalisa ko da ya bar APC.

A makon jiya kun ji cewa wani ‘Dan Majalisa da ke karkashin APC ya nemi a biya sa kudi idan har ana so ya koma PDP. ‘Dan Majalisar na Yankin Arewa ya sa kudi ne a matsayin sharadin komawa Jam’iyyar PDP mai adawa a Kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel