Sanatocin PDP sun garzaya kotu don hana majalisa tsige Saraki

Sanatocin PDP sun garzaya kotu don hana majalisa tsige Saraki

- Wasu daga cikin Sanatocin jam'iyyar PDP sun maka Sifeta Janar na 'yan sanda da shugaban hukumar DSS a kotu domin hana su yiwa Bukola Saraki barazana

- Sanatocin da suka shigar da karar su bayyana cewa canja shekar da Bukola Saraki ya yi bata tsige shi daga matsayinsa na dan majalisa ba

- Sanatocin sun kuma yi karar wasu Sanatoci da ma'aikatan majalisar da suke ganin ana iya hada baki dasu wajen tsige Saraki ba bisa ka'ida ba

Takaddamar dake afkuwa a majalisar dattawa bayan sauya shekar shugaban majalisar Bukola Saraki daga jam'iyyar APC mai mulki zuwa jam'iyyar adawa ta PDP ta dauki sabon salo bayan wasu sanotocin PDP sun shigar da kara kotu domin hana a tsige Saraki daga mukaminsa ta hanyar data sabawa doka.

Sanatocin PDP sun garzaya kotu don hana majalisa tsige Saraki

Sanatocin PDP sun garzaya kotu don hana majalisa tsige Saraki

Sanatocin da suka shigar da karar a babban kotun Abuja a jiya sun hada da Sanata Rafiu Adebayo mai wakiltan yankin kudancin Kwara da Sanata Isa Misau mai wakiltan yankin Bauchi ta tsakiya inda suke bukatar kotu ta dakatar da Ministan Shari'ah, Sufeta Janar na 'Yan sanda da Shugaban hukumar DSS daga yin wata yunkuri na tsige Saraki.

KU KARANTA: Saraki da Ekweremadu basu karfi kamu ko dauri ba - APC

Sauran sanatocin ake tuhuma da hannu wajen yunkurin tsige Bukola Saraki a karar mai lamba FHC/ABJ/CS/872/2018 sun hada da mataimakin shugaban majalisa Ike Ekweremadu, Sanata Ahmed Lawal, Sanata Bala Ibn Na'allah, Sanata Emma Buacha da Akawun majalisa da mataimakinsa.

Wanda suka shigar da karar suna bukatar kotu ta haramtawa Hukumar 'Yan Sandan Najeriya da Hukumar 'Yan Sandan Farin Hula (DSS) ikon yin barazana ga shugaban majalisa Bukola Saraki bisa takaddamar dake faruwa har sai lokacin da kotu ta yanke hukuncin kan hallarcin kasancewarsa shugaban majalisa duk da yan canja sheka ko akasin hakan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel