Shugaban masoyan Muhammadu Buhari yayi murabus daga mukamin sa

Shugaban masoyan Muhammadu Buhari yayi murabus daga mukamin sa

Shugaban kungiyar nan ta masoya Shugaban kasa Muhammadu Buhari mai suna Buhari Support Group reshen jihar Kwara, Mashood Bakare yayi murabus daga mukamin sa a hukumance.

Mashood Bakare dake yanzu haka ke zaman dan majalisar jiha dake wakiltar mazbar al'ummar Omupo na jihar ya bayyana hakan ne a zauren majalisar jihar a ranar Alhamis din da ta gabata.

Shugaban masoyan Muhammadu Buhari yayi murabus daga mukamin sa

Shugaban masoyan Muhammadu Buhari yayi murabus daga mukamin sa

KU KARANTA: Sojin Najeriya sun cafke mota makare da muggan makamai a Arewa

Legit.ng ta samu cewa haka zalika ya bayyana cewa a ajiye mukamin na sa ne don kshin kansa domin cigaba da wasu harkokin sa na rayuwa duk kuwa da rike mukamin tun shekarar 2014.

A wani labarin kuma, hadaddiyar kungiyar mabiya addinin kirista a Najeriya watau Christian Association of Nigeria (CAN) ta gargadi fadar shugaban kasa da sauran jami'an tsaro da cewa su bi ahankali kar su jefa demokradiyyar kasar cikin rikici.

Kungiyar dai ta bayyana hakan ne jim kadan bayan wani samame da sanyin safiyar jiya da jami'an 'yan sandan Najeriya suka kai a gidan shugabannin majalisar dattijai, Dakta Bukola Saraki da mataimakin sa Ike Ekweremadu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel