Masari ya nemi ma'aikatan sa kan zage dantse wajen gudanar ayyukan su

Masari ya nemi ma'aikatan sa kan zage dantse wajen gudanar ayyukan su

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, ya bayyana damuwar sa dangane da rashin kwazon ma'aikatan gwamnatin jihar sa, inda ya bayyana cewar malala ta ne gami da rashin hadin kai daga bangaren ma'aikatan musamman manya da matsakaita ga gwamnatin jihar.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin rantsar da sabon shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar sa, Alhaji Idris Usman Tuni, a fadar gwamnatin sa dake birnin Katsinan Dikko.

Masari ya nemi ma'aikatan sa kan zage dantse wajen gudanar ayyukan su

Masari ya nemi ma'aikatan sa kan zage dantse wajen gudanar ayyukan su

Alhaji Masari ya tunatar da ma'aikatan cewa, akwai babban kalubale a gaban su wajen inganta harkokin su na gudanarwa ta hanyar neman ilimi domin gogayya da 'yan uwan su ma'aikata a sassa daban-daban dake fadin kasar nan ta Najeriya.

KARANTA KUMA: Hukumar 'Yan sanda ta cafke masu Fashi da Makamin Babura a jihar Katsina

Ya ci gaba da cewa, jihar Katsina ta kere sauran jihohi ta fuskar adadi na yawan ma'aikata sai dai hakan ba ya da wani tasiri dangane da hobbasa da jajircewar su wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyan su.

Masari ya kuma nemi sabon shugaban ma'aikatan akan ya dauki salo na horas da ma'aikata a matakai daban-daban, musamman sabbin dauka aiki domin samun fa'ida ta sanin makama da kwarewar aiki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel