Dalilin da yasa APC ke farinciki da ficewar gwamna Ortom - Oshiomhole

Dalilin da yasa APC ke farinciki da ficewar gwamna Ortom - Oshiomhole

A makon da ya gabata, shugaban APC, Adams Oshiomohole, ya roki gwamna Samuel Ortom na jihar Benue kada ya fice daga jam'iyyar APC amma a yanzu bayan ya fice, sai kuma yace gwamnan dama baya tabuka komi a jihansa.

Mr Oshiomhole ya kara da cewa sauya shekar gwamna Samuel Ortom daga jam'iyyar APC zuwa PDP alkhairi ne ga APC.

A hirar da ya yi da manema labarai a ranar Juma'a, Oshiomhole yace a matsayinsa na shugaban jam'iyyar hankalinsa ya kwanta kuma yana kyautata zaton suma shugabanin APC na Benue hankulansu ya kyauta bayan Ortom ya koma kungiyar da ya fito.

Dalilin da yasa APC ke farinciki da ficewar gwamna Ortom

Dalilin da yasa APC ke farinciki da ficewar gwamna Ortom

Oshiomhole ya cacaki jam'iyyar PDP inda ya kira da "kungiyar masu rabon kudi ba tare da yiwa al'umma aiki ba".

Oshiomhole yace a yanzu suna da damar zabo dan takara mai nagarta daga jihar Benue wanda zai yiwa mutanen Benue hidima da jagoranci mai nagarata, ba wanda ya ke amfani da rayukan mutanensa don cinma wata burin siyasa ba.

Kazalika, Oshiomhole yace jam'iyyar APC tana Allah-wadai da duk wani da ke halaka mutane a jihar Benue da sauran sassan kasar.

KU KARANTA: 2019: Bangare 3 da fitar Kwankwaso zata yi tasiri a siyasar Kano

Yace jam'iyyar APC ta amince cewa nauyin kiyaye rayyuka da dukiyoyin al'umma ya rataya a kan gwamnati ne sai dai duk da haka jam'iyyar tana tir da duk wanda ke amfani da amfani da rayukan al'umma don cinma burin siyasa.

Oshiomhole yace Ortom ya gaza a matsayinsa na babban jami'in tsaro na jiharsa inda ya kara da cewa ya samu tikitin takara a jihar ne a cikin ruwan sanyi amma nan gaba jam'iyyar zata tabbatar duk wanda za'aba tikitin ya cancanta.

Ya kuma korafi kan yadda Ortom ya yi ikirarin cewa ya kashe N22 biliyan da gwamnatin tarayya ta bashi a jiharsa wajen samar da tsaro amma duk da haka har yanzu babu wata ingantaccen tsaro a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel