Neman mafaka: Tsohon gwamnan PDP ya fice daga jam’iyyar

Neman mafaka: Tsohon gwamnan PDP ya fice daga jam’iyyar

Tsohon gwamnan jihar Imo a karkashin PDP, Ikedi Ohakim, ya bayyana ficewar sa daga jam’iyya tare da komawa jam’iyyar APGA inda yake saka ran zai yi takarar gwamna a cikinta a zaben shekarar 2019.

Ohakin ya sanar da ficewarsa daga PDP ne a jiya juma’a yayin da yake jawabi ga dandazon magoya bayan jam’iyyar APGA a filin wasa na Kanu Nwankwo dake Owerri, babban birnin jihar ta Imo.

Ya ce zai yi amfani da gogewarsa a matsayin tsohon gwamna domin kawowa jihar Imo cigaban da take bukata da kuma kubutar da ita daga mulkin kama karya irin na jam’iyyar APC, kamar yadda ya fada.

Neman mafaka: Tsohon gwamnan PDP ya fice daga jam’iyyar

Ikedi Ohakim

Tsohon gwamnan ya kara da cewa a yanzu haka jam’iyyar APGA ce kadai keda mutuncin da zai iya shiga domin yin takarar neman wani mukami.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya bukaci a dakatar da yakin neman zabensa

Daga karshe ya bukaci duk ‘yan asalin jihar ta Imo dake gida Najeriya da ketare das u bashi hadin kai domin ya samu dammar cimma burinsa na kara mulkar jihar a karo na biyu tare da yi masu alkawarin zai mika mulki ga mutum mai mutunci day a fito daga Sanatoriyar Owerri da zarar ya kamala zangonsa daya na mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel