An tona asirin wani dan takarar gwamnan PDP maras takardar kammala sakandire

An tona asirin wani dan takarar gwamnan PDP maras takardar kammala sakandire

Bincike da aka gudanar ya nuna cewa Sanata Ademola Nurudeen Adeleke na jihar Osun, kuma dan takarar gwaman a karkashin jam'iyyar PDP ya yi karyar kammala karatun sakandire da kuma digiri daga jami'ar Jiha ta Jacksonville (JSU) dake Amurka.

Kamar yadda wata rahoto da icirnigeria.org ta wallafa, mahukuntar Jami'ar Jacksonville dake Jihar Alabama a Amurka sun tabbatar da cewa Adeleke ya yi rajista a jami'ar amma bai tsaya ya kammala karatun ba saboda haka bashi da digirin da ya yi ikirarin yana dashi.

Kamar yadda ya rubuta a shafinsa na Majalisar Najeriya, Adeleke yace yana da digiri a nazarin masu laifuka (criminology) daga JSU da ya kammala a shekarar 1986. Ya kuma rubuta cewa ya kammala karatun sakandire a Ede Muslim Grammar School, jihar Osun inda ya samu shedar kammalawa wato Ordinary Level.

An tona asirin wani dantakarar gwamnan PDP maras takardar kammala sakandire

An tona asirin wani dantakarar gwamnan PDP maras takardar kammala sakandire

DUBA WANNAN: Kasashe 10 da suka fi talauci a nahiyar Afirka

Sai dai cikin kwanakin nan karyata takardun karatun da ya yi ikirain ya mallaka saboda ICIR ta tabbatar cewa Adeleke bai kammala digiri daga JSU ba kamar yadda ya yi ikirari a baya.

A amsar data bayar ta sakon e-mail, direktan hulda da jama'a na JSU, Buffy Lockette, ta shaidawa ICIR cewa Sanata Adeleke ya yi rajista a jami'ar amma ba'a bashi wata shaidan digiri ba saboda bai kammala karatun ba.

A yayin da ICIR ta bincika shafin yanan gizo na WAEC domin ganin sakamakon jarabawar kammala sakandire na Sanatan mai lamba 19645/149, an tarar da cewa babu wata sakamakon jarabawa mai wannan lambar a shekarar da ya yi ikirarin ya yi jarabawar.

Shugaban sashin hulda da jama'a na WAEC, Demianus Ojijeogu, ya fadawa ICIR cewa dukkan sakamakon jarabawar daliban da suka rubuta jarabawar suna shafin yanan gizon hukumar jarabawar ko da kuwa sun fadi jarabawar ne.

Sai dai ya kara da cewa hukumar na kokarin yin gyara a shafin hukumar saboda canjin suna da su kayi daga SSCE zuwa WASC yanzu kuma sunan ya koma WASSCE, saboda haka akwai yiwuwar ba'a gama kammala saka sakamakon daliban da suka rubuta jarabawa a shekarun 1881 ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel