Jam'iyyar APC reshen jihar Edo ta bayyana dalilin hana 'Yan takara gudanar da Yaƙin neman Zabe

Jam'iyyar APC reshen jihar Edo ta bayyana dalilin hana 'Yan takara gudanar da Yaƙin neman Zabe

Jam'iyyar APC reshen jihar Edo, ta bayyana dalilin ta na hana 'yan takara masu neman tikitin jam'iyyar gudanar da duk wani nau'i na yaƙin neman zabe a fadin jihar.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, jam'iyyar ta hana manema takara gudanar da yakin neman zaben domin dakile barnatar da dukiyoyin su wajen zaben fitar da dan takara kamar yadda ya wakana a shekarar 2016 yayin zaben gwamna a jihar.

Jam'iyyar APC reshen jihar Edo ta bayyana dalilin hana 'Yan takara gudanar da Yaƙin neman Zabe

Jam'iyyar APC reshen jihar Edo ta bayyana dalilin hana 'Yan takara gudanar da Yaƙin neman Zabe

Jam'iyyar cikin wata rubutacciyar wasika da sa hannun sakataren ta na jihar, Mista Lawrence Okah ya bayyana cewa, su na kira ga dukkanin mambobin jam'iyyar akan ba ya daga cikin manufofin ta su gudanar da kowane nau'i na yakin neman zaben da manufa ta babban zaben 2019.

KARANTA KUMA: Asarar da Ambaliyar ruwa ta janyo a jihar Kebbi ta girgiza ni - Buhari

Okah cikin wasikar ta sa ya bayyana cewa, jam'iyyar ta hana gudanar da kowane nau'in gudanar da yakin neman zabe har zuwa wani lokaci na gaba.

Da yake bayanin wannan doka da jam'iyyar ta kaddamar, Okah ya bayyana cewa jam'iyyar ta cimma wannan matsaya ne domin tufke aljihun manema takara daga malalar da dukiyar su wajen neman cikar burikan su na siyasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel