Waiwaye: Harin da Boko Haram ta kaiwa soji, da satar makamai, me gwamnati ke yi?

Waiwaye: Harin da Boko Haram ta kaiwa soji, da satar makamai, me gwamnati ke yi?

- A makon jiya ma sun kashe soji yayin da suke tsakar daji kai hari a sansanin mayakan

- Boko Haram na son kafa daular Islama ta hanyar Jihadi kamar yadda Danfodio yayi

- Musulmai sun ki bin wannan akida sun zabi dimokuradiyya duk da ba ita sahabbai suka yi ba

Boko Haram ta sake kai hare-hare a wurare da dama, ta kar soji 17 da jama'a da dama, ta saci makamai

Boko Haram ta sake kai hare-hare a wurare da dama, ta kar soji 17 da jama'a da dama, ta saci makamai

A makon jiya ne, Boko Haram ta karkashe sojin Najeriya ta sace makamai, shekaru uku bayan hawan gwamnatin APC, ko ya hakan ke kara faruwa?

An dai zabo gwamnatin APC ne musamman saboda yakar Boko Haram, kuma sunyi rawar gani, sai dai hakan bai isa ba, domin korar Boko Haram daji da fatattakarsu ba cin yaki bane, zasu je zasu dawo.

Shugaba Muhammadu Buhari na iya gama shekaru hudu ya fadi zabe, kuma kamar fa a cikin 'yan siyasar nan shi kadai ne ya rage cikin 'yan mazan jiya da ka iya yaki ko tafiyar dashi, sauran yara ne ajebo, masu neman kudi da neman suna.

DUBA WANNAN: Jaddawalin Jarrabawar ma'aikatan Tarayya

Idan shugaban ya zarce kuwa, akwai sauran rina a kaba, domin wannan na nufin za'a kwashe shekaru takwas ana kashe kudade domin yakar ta'addanci, bayan kuma gashi wasu maluman na ci gaba da wa'azin mai zafaffa ra'ayin jama'a.

Bok Haram dai daga izala ta bullo, kuma ta gagari gwamnati, ta kwashi almajirai ta koya musu ta'addanci. Mahaifiyar Shekau ma a kwanan nan ta tabbatar cewa Shekau Almajiri ne da babansa limamin kauye ya kai gabas karatu.

Tun zamanin Usmanu Danfodio ake wannan jihadi, ake kuma samar da mayaka daga cikin Almajiirai, ko yaushe hakan zai tsaya?

Ya zuwa yanzu dai, a iya cewa shekaru uku sun isa ace an gama da Boko Haram, kamar yadda aka sa rai a 2015. Duk da cewa an yi namijin kokari wajen korarsu daji, hakan bai sa an iya binsu daji an gama dasu ba, wai sai dai a kore su.

Sharhin Mubarak Bala. Ba lallai ra'ayin jaridar Legit.ng ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel