Wasu Mutane 2 sun tsallake Rijiya da baya yayin da Kwantena ta rufta kan Motocin su a jihar Legas

Wasu Mutane 2 sun tsallake Rijiya da baya yayin da Kwantena ta rufta kan Motocin su a jihar Legas

A ranar da ta gabata ne direbobin wasu motoci biyu kirar Sienna da Camry, sun tsallake rijiya da baya yayin da wata katafaiyar kwantenar kaya ta rufta kan motocin su a tashar jiragen ruwa ta Tin-Can Island dake garin Apapa can jihar Legas.

Wani mashaidin wannan tsautsayi ya bayyana cewa, wannan babbar kwantenar ta daukan kaya ta fado kan motocin biyun ne yayin da ake jigilar ta daura da shatale-shatalen dake tsakanin gadar Apapa da tashar jiragen ruwan ta Tin-Can.

Wasu Mutane 2 sun tsallake Rijiya da baya yayin da Kwantena ta rufta kan Motocin su a jihar Legas

Wasu Mutane 2 sun tsallake Rijiya da baya yayin da Kwantena ta rufta kan Motocin su a jihar Legas

Rahotanni sun bayyana cewa, ganganci daga bangaren direban motar dake jigilar wannan kwantena ne ya yi sanadiyar aukuwar wannan mummuna hatsari.

KARANTA KUMA: Sanata Hunkuyi ya bayar da Hakuri na barin jam'iyyar PDP a 2015

A yayin da direbobin kananan motocin biyu dake karkashin gadar ta Apapa suka hangi jirkicewar kwantenar, ya sanya cikin razani da gaggawa suka tsere tare da barin Motocin nan take sakamakon jerin gwanon motocin da aka saba kamar kullum cikin birnin Legas.

Kamar yadda shafin jaridar Vanguard ya bayyana, wasu jami'an tsaro na 'yan sanda, sojin kasa da kuma ma'aikata na hukumar bayar da agajin gaggawa ta LEMA (Lagos State Emergency Management) sun shiga cikin lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel